SMART HUB 24

Technology • News • Security

Abubuwa 7 da Ya Kamata Kowane Mai Wayar Android Ya Yi Domin Kare Bayanansa

Abubuwa 7 da Ya Kamata Kowane Mai Wayar Android Ya Yi Domin Kare Bayanansa

Technology & Cyber Security


Gabatarwa;

A yau, wayar Android ta zama wani ɓangare na rayuwarmu. Muna amfani da ita wajen ajiye hotuna, shiga banki, hanyoyin sadarwa kamar WhatsApp, domin  gudanar da kasuwanci. Amma abin da mutane da yawa ba su sani ba shi ne, idan ba a kiyaye tsaro ba, masu kutse za su iya samun damar shiga bayananka cikin sauƙi.

Abin farin ciki shi ne, ba sai ka zama ƙwararren masani ba kafin ka kare bayanan wayarka. Akwai matakai masu sauƙi da za su taimaka wajen rage haɗarin kutsen  bayanai.

1. Kariƙa Sabunta Application Lokaci-Lokaci (Update);

Sabuntawa ba wai don yana ƙara sabbin fasaloli kawai ba ne. Yawanci suna gyara matsalolin tsaro da masu kutse za su iya amfani da su.

Sannan a duba Settings > System > Software Update akai-akai.

2. Sauke Application Marasa Asali;

Yawancin malware na shiga waya ne ta hanyar APK daga shafukan da ba a sani ba.

Domin gujewa hakan yi amfani da

.Google Play Store

.Shafukan hukuma na kamfanoni

Ka guji sauke apps daga hanyoyin da ba ka yarda da su ba.

3. Yi Amfani da Kalmar Sirri Mai Ƙarfi;

PIN mai sauƙi kamar 1234 ko 0000 yana da sauƙin ganewa.

Ka fi amfani da:

. PIN mai tsawo

. Password mai ƙarfi

. Fingerprin

. Face Unlock (idan wayarka tana da shi)


4. Kunna Two-Factor Authentication (2FA);

Asusunka na Gmail, Facebook, WhatsApp da sauran apps ya kamata su kasance da 2FA.

Ko da wani ya san kalmar sirrinka, ba zai iya shiga ba sai ya samu lambar tabbatarwa daga 2FA.

5. Ka Guji Free  Wi-Fi na Jama'a Ba Tare da Kulawa Ba;

Free Wi-Fi na kyauta a wasu wurare na iya zama haɗari. Wasu masu kutse kan ƙirƙiri Free don  sadarwa na bogi domin satar bayanan mutane.

Idan dole ne ka yi amfani da irin wannan Wi-Fi, to ka tabbayar haka shiga bank App  ba ko saka kalmomin sirri awurare masu muhimmanci.

6. Ka Duba Izinin (Permissions) da Apps Ke Nema:

Ba kowane app ne yake buƙatar damar shiga:

. Camera

. Microphone

. Contacts

. Location

Ka duba izinin da ka ba apps, sannan ka cire wanda ba su dace App din su samu permission ba musaman App marasa Asali.

7. Yi Backup na Muhimman Bayananka;

Ka adana hotuna, takardu da lambobin waya a Google Drive ko wani wuri mai aminci.

Idan wayarka ta lalace ko aka sace ta, za ka iya dawo da bayananka cikin sauƙi.

Tsaron wayarka yana farawa ne daga matakan da kake ɗauka kullum. Ƙananan abubuwa kamar sabunta software, amfani da kalmar sirri mai ƙarfi da guje wa apps marasa aminci na iya kare bayananka daga barazanar masu kutse Hackers.

Ka tuna, kare bayananka ya fi sauƙi fiye da ƙoƙarin dawo da su bayan sun shiga hannun da bai dace ba.

Masha Allah 

Muktar Hassan

Welcome to SMART HUB 24, your trusted source for news, education, technology, and business insights. We provide valuable content in Hausa and English to inform, educate, and inspire our readers."

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post