Yadda Zaka Mayar Da Basirar Da Allah Ya Baka Hanyar Samun Kuɗi – Kashi Na 4
Gabatarwa:
A kashi na baya mun tattauna kusakuran da ke hana matasa cin moriyar baiwar da Allah Ya ba su. Yanzu tambaya ita ce: Ta yaya za ka mayar da wannan baiwa ta zama hanyar samun kuɗi da ci gaba?
Ka sani, basira ba kawai don nishaɗi aka ba ka ita ba. Idan aka inganta ta kuma aka yi amfani da ita yadda ya kamata, za ta iya zama hanyar samun abin dogaro da kai.
Mataki na 1:
Ka tambayi kanka:
Wane aiki nake yi cikin sauƙi?
Wane abu mutane suke yawan yaba min a kai?
Wane aiki nake jin daɗin yi ko da ba a biya ni ba?
Mataki na 2:
Ƙara Ilimi da Ƙwarewa
Basira kaɗai ba ta wadatar. Ka nemi ilimi ta hanyar:
Karanta littattafai.
Kallon bidiyoyin koyarwa.
Halartar guraren training da kwasa-kwasai.
Koyon sababbin dabaru.
Mataki na 3:
Fara Da Abin Da Kake Da Shi
Kada ka jira komai sai ya cika. Idan kana da waya, ilimi, ko ƙaramin jari, ka fara da su. Babbar narara Aiki yana bunƙasa ne mataki-mataki.
Mataki na 4:
Bayyana Ayyukanka Ga Mutane
Yi amfani da kafafen sada zumunta ko website domin nuna abin da kake iya yi. Idan mutane ba su san ƙwarewarka ba, ba za su nemi aikinka ba.
Mataki na 5:
Ka Kasance Mai Aminci da Haƙuri
Nasara tana buƙatar lokaci. Ka kasance mai gaskiya, mai haƙuri, kuma ka ci gaba da inganta aikinka.
Akarshe:
Allah Ya ba ka baiwa saboda wata hikima. Idan ka haɗa basira da ilimi, aiki tukuru, da tawakkali ga Allah, akwai damar ta zama hanyar samun kuɗi da gina rayuwa mai kyau.
A Kashi Na 5
Za mu tattauna:
"Yadda Zaka Gina Sunanka Da Martabarka Ta Hanyar Basirarka."