Yadda Zaka Gano Basirar Da Allah Ya Baka
Menene basira?
Alamomin da ke nuna kana da basira
Me yasa mutane da yawa basa gane basirarsu?
Kashi na 1:
Yadda Zaka Taimaki Kanka Da Basirar Da Allah Ya Baka Domin Samun Nasara A Rayuwa
Allah Ya halicci kowane mutum da wata baiwa ko basira ta musamman. Wasu suna iya koyarwa, wasu rubutu, wasu kasuwanci, wasu kuma fasahar zamani. Amma abin takaici, mutane da yawa suna rayuwa ba tare da sun gano baiwar da Allah Ya ba su ba.
1. Ka Gano Basirarka
Mataki na farko shi ne ka tambayi kanka:
Wane aiki nake yi cikin sauki?
Wane abu mutane suke yabona a kai?
Wane aiki nake yi ba tare da gajiya ba?
Amsoshin wadannan tambayoyi na iya taimaka maka gano baiwar da Allah Ya baka.
2. Ka Koyi Sabbin Abubuwa
Basira kadai ba ta isa ba. Kana bukatar ilimi da horo domin bunkasa ta. Karanta littattafai, kalli bidiyoyin koyarwa, kuma ka nemi shawarwari daga masana.
3. Ka Daina Dogaro Da Wasu
Mutane da yawa suna jiran wani ya taimake su kafin su fara aiki. Amma mafi yawan masu nasara sun fara ne da abin da suke da shi.
4. Ka Yi Hakuri
Nasara ba ta zuwa cikin dare daya. Ka dage, ka yi kokari, ka yi addu'a, sannan ka ci gaba da aiki.
5. Ka Amfani Da Fasaha
A wannan zamani, wayar hannu kadai na iya zama hanyar samun kudi idan aka yi amfani da ita yadda ya dace. Rubuce-rubuce, koyarwa, kasuwanci da sauran ayyuka suna samuwa a yanar gizo.
Kammalawa
Kada ka raina baiwar da Allah Ya baka. Wata karamar basira da kake da ita ce za ta iya canza rayuwarka gaba daya idan ka yi amfani da ita yadda ya kamata. Ka fara yau, ka yi aiki da abin da kake da shi, Allah zai sanya albarka.