SMART HUB 24

Technology • News • Security

Yadda Zaka Gano Basirar Da Allah Ya Baka - Kashi Na 2: Alamomi 7 Da Ke Nuna Kana Da Baiwa Ta Musamman

Yadda Zaka Gano Basirar Da Allah Ya Baka - Kashi Na 2: Alamomi 7 Da Ke Nuna Kana Da Baiwa Ta Musamman

Ga Alamomi 7 da ke Nuna Kana da Baiwa Ta Musamman

Kashi na 2:

1. Kana yin wani abu cikin sauƙi fiye da sauran mutane:

Akwai wasu ayyuka da kake yi ba tare da wahala ba, alhali wasu suna ganin suna da wahala. Wannan na iya zama baiwar da Allah Ya ba ka.

2. Mutane suna yawan yaba maka a abu 1:
Idan mutane suna yawan cewa kana da ƙwarewa a wani fanni, kada ka yi watsi da hakan. Sau da yawa hakan alama ce ta kana da baiwa.

3. Kana jin daÉ—in yin wani aikin ba tare da gajiya ba:
Idan kana iya shafe wani muhimmin  lokaci kana yin wani aikin ba tare da ka gaji  ba, wannan na  nuna cewa kana da baiwa a wannan fannin.

4. Kana saurin koyon  abu:
Idan kana saurin fahimta da koyon wani abu fiye da sauran mutane, wannan alama ce ta baiwa ta musamman.

5. Kana samun sababbin dabaru akai-akai:
Kana yawan tunanin hanyoyi ko dabaru da za su inganta abin da kake yi. Wannan yana nuna cewa Allah Ya ba ka basirar kirkire-kirkire.

6. Kana jin kamar an halicce ka domin wani aiki:
A zuciyarka kana jin wannan fanni ya dace da kai kuma kana jin natsuwa idan kana aikata shi.

7. Ayyukanka suna amfani ga mutane
Idan abin da kake yi yana taimakon mutane kuma suna amfana da shi, akwai yiwuwar wannan ita ce baiwar da Allah Ya hore maka.

Masha Allah. Muna Tafe da Kashi Na 3 Insha Allah 
Muktar Hassan

Welcome to SMART HUB 24, your trusted source for news, education, technology, and business insights. We provide valuable content in Hausa and English to inform, educate, and inspire our readers."

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post