Sojoji Sun Samu Nasarar Ceto Mutane Biyu Daga Hannun Masu Garkuwa a Benue

Sojoji Sun Samu Nasarar Ceto Mutane Biyu Daga Hannun Masu Garkuwa a Benue

Dakarun Sojojin Najeriya sun ceto mutane biyu daga hannun waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Jihar Benue.

An gudanar da aikin ceton ne a ranar 24 ga Oktoba, 2026, a kan hanyar  Ahume, ƙarƙashin rundunar soji ta Operation Whirl Stroke.

Rahoton Leadership Hausa ya bayyana cewa sojojin sun yi musayar wuta da waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne, lamarin da ya sa suka gudu suka bar mutanen.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto, mai suna Mngunengen Ihom, mai shekaru 36, ta samu raunuka sakamakon sara da adda.

An kai ta Babban Asibitin  domin samu ta samu kulawar likitoci. Har zuwa lokacin da rahoton ya fito, rundunar ba ta bayyana sunan mutum na biyu da aka ceto ba.

Comments