Yadda Ake Buɗe Facebook Account: Cikakken Bayani Zuwaga Masu Farawa.
Cikekkiyar Gabatarwa
Facebook na ɗaya daga cikin manyan kafafen sada zumunta da ake amfani da su a duniya. Yana ba wa mutane damar sadarwa da zumunta, abokai, da kuma samun damar kasuwanci.
Haka kuma, ana amfani da shi wajen karanta labarai, kallon bidiyo, shiga kungiyoyi, da tallata kayayyaki da ayyuka.
Idan ba ka taɓa buɗe Facebook Account ba, acikin wannan post zai jagoranceka yadda ake budewa cikin sauƙi.
Menene Facebook Account?
Facebook Account shi ne asusun da ke ba ka damar shiga Facebook domin amfani da dukkan ayyukansa. Da zarar ka ƙirƙiri account, za ka iya:
Tura saƙonni (Messenger).
Sanya hotuna da bidiyo.
Shafuka (Facebook Page).
Buɗe Facebook Page domin kasuwanci.
Abubuwan da Za Ka Buƙata Kafin ka fara, ka tabbata kana da:
Wayar hannu ko kwamfuta.
Sai Intanet.
Lambar waya ko Gmail.
Cikekken Sunan ka.
Ranar haihuwarka.
Mataki na 1:
Je Shafin Facebook ko browser ɗinka sannan ka shiga:
Ko kuma ka sauke Application na Facebook daga Google Play Store ko Apple App Store.
Mataki na 2: Danna "Create New Account"
A shafin farko za ka ga Create New Account.
Danna shi domin rajista.
Mataki na 3: Cika Bayanan Ka
Facebook zai buƙaci ka shigar da:
Sunan ka na yanka.
Sunan mahaifi.
Ranar haihuwa.
Jinsi (Male ko Female).
Lambar waya ko Gmail.
Kalmar sirri (Password).
Note:
Ka tabbata password ɗinka yana da tsauri kuma kada ka sanar kowa.
Mataki na 4: Tabbatar da Account;
Facebook zai turo maka lambar tabbatarwa (OTP) a ta number layin ko Gmail kaitsaye.
sai ka rubuta lambar domin tabbatar da cewa kai ne mai account ɗin.
Mataki na 5: Saka Hoton Profile
Bayan an buɗe account ɗinka, za ka iya saka:
Hoton profile.
Hoton cover.
Bayanin kanka.
Wanda hakan zai sa mutane su gane account ɗinka cikin sauƙi.