Beep Call
Beep" ko Flash Call yana faruwa ne idan mutum ya kira ka sannan ya katse kiran kafin ka É—aga.
A wasu lokutan kuma, mutane suna yin haka ne idan ba su da isasshen kuÉ—in kira ko kuma suna son ka kira su.
Kamfanonin sadarwa ba su ƙirƙiri beep a matsayin sabis na musamman ba. Sai dai ansamar dashi ne saboda tsarin cibiyar sadarwa da ke nuna missed call.
Wanda daga baya, mutane suka mayar da shi wata hanya ta sadarwa.
A yau, ana amfani da beep wajen sanar da mutum cewa:
- Ka kira ni.
- Na iso wani wuri.
- Ina bukatar kulawa.
dss.
Duk da yake beep yana da amfani, idan saƙo yana da muhimmanci, kira kai tsaye ko tura saƙon rubutu shi ne mafi dacewa.
Kuyi mana Share Don Allah