An buɗe shafin ɗaukar sabbin ma'aikata na Hukumar Kare Hadurra ta Najeriya (FRSC). Wannan dama ce ga matasa masu neman aikin gwamnati domin su nemi guraben aiki ta hanyar cike form ɗin da aka tanada a shafin.
Mene ne FRSC?
Federal Road Safety Commission (FRSC) hukuma ce ta gwamnatin tarayya da ke da alhakin tabbatar da tsaro da kiyaye dokokin zirga-zirga a manyan hanyoyin Najeriya. Haka kuma tana taimakawa wajen rage haɗurran mota da ceton rayuka.
Yadda Ake Cike Form
Danna link kaitsaye : https://recruitment.frsc.gov.ng�
Cika duk bayanan da ake buƙata daidai.
Idan kana da sha'awar aikin gwamnati, kada ka bari wannan dama ta wuce ka. Ka cika form a wannan lokaci kuma ka tanadi duk takardun da ake buƙata.
Daukar ma'aikatan FRSC na 2026 wata dama ce mai kyau ga matasan Najeriya.