1. A hotunan da kuke gani, duka suna nuni ne a wani ɓangare na yadda hukumomin tsaro ke amfani da fasahar zamani wajen gudanar da ayyukan Intelligence, Surveillance and Reconnaissance (ISR). Wannan fasaha tana taimakawa wajen sa ido, tattara bayanan sirri da kuma bibiyar waɗanda ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci, musamman a yankunan dazuka da wuraren da ke da wahalar isa.
2. Jiragen ISR suna ɗauke da na’urori masu ƙarfi kamar:
Electro-Optical (EO) Cameras
Infrared/Thermal Imaging Sensors
Na’urorin tattara bayanan sirri daga nesa
Waɗannan na’urori suna bai wa jami’an tsaro damar sa ido kan abubuwan da ake zargi ba tare da kusantar su kai tsaye ba.
3. Yadda Thermal Imaging ke Aiki
Ɗaya daga cikin manyan fasahohin da ake amfani da su a ISR ita ce Thermal Imaging Technology. Wannan fasaha tana gano zafin da jikin mutum ko wata halitta ke fitarwa.
Saboda haka, ko da cikin duhu ko daji mai girma ne, mutum na iya bayyana a sannan kuma jamian sa ido Suma su ganshi a matsayin wani haske mai motsi. Hakan yana sauƙaƙa ganowa da bibiyar waɗanda ake zargi ba tare da sun san ana sa ido a kansu ba.
Amfanin ISR a Ayyukan Tsaro
Da zarar an gano motsin waɗanda ake zargi, tsarin ISR na iya samar da sahihan bayanai game da inda suke cikin ɗan lokaci kaɗan. Wannan yana bai wa jami’an tsaro damar gano wuraren da ake zargin maƙiya da bata gari suke.
4. Bibiyar motsinsu.
Tattara bayanan sirri kafin fara aiki.
Rage haɗarin da jami’ai ke fuskanta yayin gudanar da ayyuka.
Zuwan Fasaha Ta Sauya Salon Yaƙi Mutuƙa
A zamanin yau, nasara a yaƙi ba ta ta’allaka ne ga ƙarfin makamai kawai ba. Maimakon haka, tana ƙara dogaro da samun ingantattun bayanai da amfani da fasahar zamani.
5. Drones, jiragen ISR da sauran na’urorin tattara bayanan sirri sun zama muhimman kayan aiki wajen:
Gano maƙiya dama ƴen Taaddan daji.
1.Kare rayukan jami’an tsaro.
2.Inganta tsare-tsaren yaƙi.
3.Ƙarfafa tsaron ƙasa.
Akarshe
Fasahar ISR ta nuna yadda yaƙi da matsalolin tsaro ya sauya daga dogaro da makamai kawai zuwa amfani da bayanai da fasaha. Mutum na iya kasancewa cikin daji ko cikin duhu yana tunanin babu wanda yake ganinsa, alhali kuwa ana iya bibiyarsa daga sama ta hanyar na’urorin zamani masu gano zafin jiki, tantance motsi da kuma tattara bayanan sirri a ainihin lokacin da yake motsawa.
Allah Ya tabbatar da zaman lafiya a ƙasarmu tare da kare rayukan al’umma da jami’an tsaro.